Isra’ila Ta Kai Manyan Kayan Yaki Kan Iyakar Lebanon

Joseph Aoun: Muna Jiran Amsar  Tattaunawa Da Isra'ila!
13 Nuwamba 2025 - 11:08
Source: ABNA24
Isra’ila Ta Kai Manyan Kayan Yaki Kan Iyakar Lebanon

Yayin da gwamnatin Sihiyona ke ci gaba da kai hare-haren wuce gona da iri kan Lebanon, kafofin watsa labaran gwamnatin sun wallafa hotunan mika kayan aikin soja da tankunan sojoji zuwa iyakar Lebanon.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na AhlulBaiti (As) –ABNA-ya habarta cewa: majiyoyin Isra’ila sun ruwaito cewa gwamnatin tana aika da kayan aikin soja da yawa zuwa iyakokin arewa da Lebanon.

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Falasdinu "Sama", ya kawo cewa: wasu kafofin watsa labaran Isra’ila sun yada wani fim na mika tankoki da kayan aikin soja zuwa iyakar Lebanon.

A gefe guda kuma, kamfanin dillancin labarai na "Al-Ahed" ya ruwaito cewa wani jirgin sama mara matuki na Isra’ila ya tashi a kan wani wuri mai nisa a kan yammacin Bekaa.

Sake take hakkin ikon Lebanon da gwamnatin Isra’ila ta yi ya biyo bayan shiru mai tayar da hankali daga al'ummomin duniya kuma ya kara nuna damuwa game da kai hari kai tsaye ga fararen hula da kayayyakin more rayuwa na birane.

Gwamnatin Isra’ila ta fara kai hare-harenta kan Lebanon a ranar 1 ga Oktoba, 2024, kuma bayan watanni 2, a ranar Laraba, ta sanya hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta tare da shiga tsakani na Amurka, amma ta karya ta sau dubbai.

A cewar yarjejeniyar tsagaita wuta, sojojin gwamnatin Isra’ila za su janye daga kudancin Lebanon cikin kwanaki 60, amma gwamnatin, sabanin dokokin kasa da kasa, ta ajiye sojojinta a wurare biyar na dabarun yaki a wannan yanki kuma ba ta tafi ba.

Shugaban Lebanon: Muna Jiran Martanin Isra'ila Don Fara Tattaunawa Da Isra’ila

Tare da wadannan motsi, Shugaban Lebanon Joseph Aoun ya sanar da cewa kasarsa tana jiran martanin gwamnatin Isra’ila don fara tattaunawa.

Yana jaddada cewa tattaunawa ita ce hanya daya tilo ta cimma burin kasar Lebanon, ya kara da cewa: Gwamnatin Lebanon ta dage kan hanyar diflomasiyya da tattaunawa.

Aoun ya kuma bayyana cewa: "Ni da Firayim Minista da Shugaban Majalisar Dokoki, duk mun dage kan gudanar da zaben 'yan majalisa a kan lokaci, kuma wannan batu yana daya daga cikin manyan abubuwan da gwamnati ta sa gaba".

Shugaban Lebanon ya ci gaba da yin watsi da wasu daga cikin tuhumetuhume yana mai cewa: "Hizbullah ba ta da hannu a yankin da ke kudu da Kogin Litani, kuma sojojin Lebanon suna gudanar da ayyukansu da ƙarfi a kudanci da sauran yankunan ƙasar".

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha